
A babban taron watan Safar karo na 18 a Abuja, an gabatar da muhimmin bayani kan yadda koyarwar Manzon Rahama ke zama mafita ga matsalolin duniya.

Taron watan Safar karo na 18 da ya gudana a birnin Abuja ya karkare tare da gabatar da cikakken bayani kan muhimmancin komawa ga koyarwar Manzon Allah (SAW) domin kawo karshen zalunci da rarrabuwar kai.
Jawabin ya bayyana cewa sakon da Manzon Allah ya zo da shi ba na zamani daya ba ne, tsari ne na rayuwa da ke tabbatar da 'yanci, mutunci, da zaman lafiya ga daukacin bil'adama.
"Hanyar samun tsira a duniya da lahira ita ce riko da dabi'un Manzon Rahama da tsayawa tsayin daka wajen kare hakkin wanda ake zalunta," inji jawabin.
An bukaci mahalarta taron da su yi amfani da irin wadannan taruka wajen karfafa zumunci tsakanin al'umma da kuma kin amincewa da duk wani yunkuri na rarraba kawuna.




