
A yayin babban taron mata a Abuja, an bayyana muhimmancin juriya da kuma rawar da mata ke takawa wajen gina al'umma da kare hakkin bil'adama.

An gudanar da gagarumin taron mata shugabanni da masu fafutukar ci gaban al'umma a birnin Abuja, inda aka tattauna kan hanyoyin karfafa tarbiyya da dorewar adalci a cikin al'umma.
An bayyana a wurin taron cewa duk wata barazana ko tsangwama ba za ta taba kawar da gaskiya ba, domin addinin Allah yana cikin zuciyar al'umma.
"Tarihi ya tabbatar da cewa duk lokacin da aka yi kokarin murkushe gaskiya da karfi, hakan yana kara fito da kyawunta ne da kuma karfafa zukatan masu neman adalci."
An jinjina wa matan da suka tsaya tsayin daka wajen ba da kyakkyawar tarbiyya da tallafa wa marayu da masu rauni, tare da kiran su da su ci gaba da neman ilimi mai zurfi domin amfanar al'umma.




