
A wani taron karawa juna sani a Abuja, an bayyana yadda tsarin jari-hujja na kasashen yamma ya gaza, da kuma bukatar komawa ga adalci domin samun 'yancin Afirka.

An gudanar da babban taron karawa juna sani a birnin Abuja tare da masana da manazarta kan hanyoyin kawo karshen mulkin mallaka da dogaro da kai a nahiyar Afirka.
An bayyana a wurin taron cewa tsarin tattalin arziki na jari-hujja bai haifar wa kasashen Afirka komai ba sai bashin kasashen waje da sace arzikin kasa.
"Ba za a taba samun cikakken 'yanci ba har sai kasashen Afirka sun koma ga dogaro da kai da kuma riko da koyarwar addini mai kafa adalci ga kowa."




