
Darasi na musamman ga malamai a Abuja kan cewa biyayya ga Manzon Allah da Ahlul Baiti tana tabbata ne ta hanyar kyawawan ayyuka da gaskiya.

A wani taron karawa juna sani na malamai da masu wa'azi a Abuja, an gabatar da cikakken bayani kan yadda soyayya ga Iyalan Gidan Manzon Allah (SAW) take bayyana a aikace.
An bayyana cewa ba a gane mai son Ahlul Baiti a baki kadai ba, ana gane shi ne a kasuwa wajen gaskiyar ciniki, a unguwa wajen kyakkyawar mu'amala, da kuma wajen tsayawa kan gaskiya.
"Koyarwar Ahlul Baiti tana bukatar mutum ya zama abin alfahari ga addininsa ta hanyar rikon amana, taimakon mabukata da yaki da zalunci."
article.noRelatedArticles